Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Yarjejeniyar tsagaita wuta na sake rauni a Ukraine

Kasar Ukraine ta fatattaki wasu ‘yan tawayen da ke goyon bayan Rasha bayan sun kai wani hari tare da yin amfani da tankokin yaki. Lamarin da ke barazana ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar.

REUTERS/Valentyn Ogirenko
Talla

Yarjejeniyar tsagaita wutar dai na sake rauni, yayin da ‘yan tawayen suka kaddamar da harin da ake ganin zai iya tsananta riikicin da aka kwashe watanni 16 ana yi tun bayan ballewar yankin Crimea daga Ukraine a kokarinsu na hade wa da Rasha.

Shugaban Kasar ta Ukraine Petro Poreshenko ya bayyana cewa, kimanin 'yan tawaye 200 ne suka yi amfani da tankokin yaki tare da kutsawa cikin garin Novolaspa a sanyin safiyar yau kuma sun ritsa da dakarun gwamanti da ke aikin tsaro a yankin.

Shugaban hafsoshin tsaron Kasar Janar Viktor Muzhenko ya shaidawa Poreshenko cewa, dakaraun Ukraine sun fatattaki ‘yan tawayen duk da harin ba zatan da suka kai.

Wata Sanarwa da Ma’ikatar tsaron kasar ta fitar ta ca, lura da yin fatali da yarjejeniyar tsagaita wutar, ‘yan tawayen na ci gaba da tayar da kayar baya wanda kuma zai tsananata rikicin da kasar ta tsinci kanta a ciki.

To sai dai 'yan tawayen sun musanta cewa dakarun gwamanati sun fattattake su kuma sun ce suna da sansanoni a garin na Novolaspa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.