Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Ukraine ta talauce sakamakon fada da ‘yan tawaye

Rahotanni daga kasar Ukraine na cewar kasar ta karaya sakamakon yakin da take tafkawa da mayakan ‘yan tawaye masu goyon bayan kasra Rasha

A woman walks out of her damaged house in the town of Debaltseve, north-east from Donetsk, March 17, 2015.
A woman walks out of her damaged house in the town of Debaltseve, north-east from Donetsk, March 17, 2015. REUTERS/Marko Djurica
Talla

Yanzu haka dai an ce kasar ta kariye ne ta bangaren tattalin arziki kan abubuwan da suka shafi zagayawar kudi tsakanin a l’umma, da kasafin kudi na gwamnati da Kamfunna da Masana’antu da Bankuna da kuma bangaren samar da Hasken Lantarki.

Wannan matsalar dai kan iya haddasa kasar ta Ukraine ta dogara kacokan ga neman tallafin kassahen waje.

Dakarun kasar Ukraine dais un kasance suna tafka kazamin fada da mayakan ‘yan tawayen na yankin gabashin kasar da kuma ke samun goyon bayan kasar Rasha wadda kasashen Turai suka y iwa taron dangi.

Kassahen Turai da Amurka dai na kallon Rasha a matsayin wacce ke ruwa-tsaki ga tashin hankalin na kasar Ukraine ne, inda har suka kakaba mata Takunkunman karya tattalin arziki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.