Isa ga babban shafi
Ukraine

Putin na kokarin mamaye Turai, inji Poroshenko

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya zargi Shugaban Rasha Vladimir Putin da kokarin mamaye Turai, shugaban ya fadi haka ne a zantawarsa da RFI.

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko
Shugaban Ukraine Petro Poroshenko REUTERS/Mykola Lazarenko/Ukrainian Presidential Press Service/Ha
Talla

Poroshenko ya shaidawa RFI cewa idan aka sa ido Putin zai mamaye wasu kasashen Turai bayan Ukraine.

Shugaban ya ce lura da ballewar yankin Crimea da kuma rikicin da kan ikon gabashin kasar ya tabbatar da Rasha na kokarin mamaye Ukraine ne.

Shugaban kuma ya danganta rikicin tsakanin dakarun Ukraine da ‘Yan tawaye da Rasha ke goyon baya ya shafi Turai baki daya.

Poroshenko kuma ya zargi Rasha da kokarin abkawa Finland da wasu kasashen yankin Balkans.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.