Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka na shirin jigbe Makamai a Turai akan Rasha

Kasar Amurka ta bayyana aniyarta na jibge manyan makamanta a yankin gabashin nahiyar Turai, a wani mataki na wucin gadi karkashin kungiyar tsaro ta NATO, saboda barazanar Rasha akan rikicin Ukraine.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ne ya bayyana haka a jiya Talata a birnin Tallinn na kasar Estonia, inda ya ce suna shirin jibge makaman ne a matsayin wucin gadi, wadanda suka suka hada motocin yaki.

Wannan sanarwa tazo ne a daidai lokacin da rikici tsakanin dakarun kasar Ukraine da ‘yan tawaye ke samun goyon bayan kasar Rasha da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 6,400 tun cikin watan Afrilun 2014.

Rikicin na kokarin rikidewa zuwa na manyan kasashen duniya

Ministocin harakokin wajen kasar Rasha da Ukraine da Faransa da Jamus a jiya Talata sun yi wata ganawa a birnin Paris, inda suka tattauna kan yadda za a farfado da aiki da yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Minsk a kasar Ukraine, kwana guda bayan da kungiyar Tarayyar turai ta kara tsawaita takunkuman kariyar tattalin arzikin da ta kakabawa kasar Rasha, kan rawar da ta ke takawa a cikin rikicin kasar Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.