Isa ga babban shafi
Faransa-EU-Jamus

Hollande ya ce Karshan Turai na gab da Zuwa

Shugaban Faransa Francois Hollande wanda ke gabatar da jawabi irinsa na farko a zauran Majalisar Turai, ya yi gargadi cewa Turai na gab da kawo karshanta mudin shugabanni Nahiyar suka nu na gazawarsu wajen magance kwararar Bakin haure.

Shugaban Faransa Francois Hollande a zauren Majalisar Kungiyar kasashen Turai
Shugaban Faransa Francois Hollande a zauren Majalisar Kungiyar kasashen Turai REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Karon farko tun bayan shekarar 1989 da Shugaban Gwamnatin Jamus da na Faransa ke gabatar da jawabai a zauran majalisar Turai, kuma a wannan karon sun mayar da hankali ne kan hanyar samar da maslaha fitittuni da ke adabar Nahiyarsu.

Shugaban na Faransa Francois Hollande ya jadada cewa sakaci Kasashen Turai da nuna jan kafa wajen bulo da hanyar dakile rikicin gabas ta tsakiya da wasu sassan Afrika su ne a yau suka haifar da tuturuwar bakin haure da ke barazana kawo karshan Nahiyar Turai.

Hollande ya ce yakin Syria, ba wai gabas ta tsakiya kawai ya shafa ba, hada Turai, domin yin zuru ba na turai ba ne, sai dai kuma ya yi kaukausar soka kan Rasha da a yanzu hare-harenta ke sake zafafa a Syria

Ana ta bangaren kuwa Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi dokokin Kungiyar kasashen Turai kan Bakin haure na tatare da kura-kurai, abin da ke baiwa kowacce kasa daman karban Bakin haure kai tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.