An baiwa 'yan gudun hijira da suka je Jamus tsare tsare zama a birnin Berlin
Yau Laraba wasu jaridun kasar Jamus suka buga wasu jerin tsare tsaren zama, ga ‘yan gudun hijiran dake zaune a Berlin, babban birnin kasar. Dama dai kafaffen yada labarun Jamus sun bayyana goyon bayansu ga matakin da mahukuntan kasar suka dauka, na dube kofofi ga ‘yan gudun hijira dake tserewa yake yaken da ake yi a Syria da Iraqi.
Wallafawa ranar:
Jaridun Bild da BZ ne suka wallafa jerin tsare tsaren, masu shafuka 4, da aka rubuta cikin harshen Larabci, da kuma suka yiwa taken Maraba da zuwa Berlin.
Tsare tsaren, masu shafuka 4, sun kunshi taswirar dake dauke da fassarar sunayen muhimman yankunan birnin, da matsugunan ‘yan gudun hijira da sauran ofisoshin jami’an shige da ficen jama’a.
Tsare tsaren da aka buga a jaridun na yankin Berlin, sun kuma kunshi Kamus na muhimman jumlolin harshen Jamusanci, gaishe gaishe da ranakun mako.
Jaridar BZ ta nemi masu karatu su bayar da bugun na yau laraba, a masayin kyata ga ‘yan gudun hijira, bayan sun gama karantu.
Dama a baya bayan nan Bild, da tafi kowacce jarida kasuwa a Jamus, tayi ta yin wani gangamin da ta kira MUNA TAIMAKAWA, dake kokarin wayar da kanun ‘yan kasar su karbi ‘yan gudun hijiran.
Jamus, da tafi kowacce kasa karfin tattalin arziki a nahiyar Turai, na sa ran karbar masu neman mafaka, su fiye da 800,000, cikin wannan shekarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu