Isa ga babban shafi
TARAYYAR TURAI-BAKIN-HAURE

Dubban yan gudun hijirar kasar Syriya sun samu tarba a kasashen Jamus da Austria

A jiya assabar dubun dubatar yan gudun hijirar kasar Syriya da suka fito daga kasar Hongri ne, suka taru a kasashen Austria da Jamus, a daidai lokaci da matsalar kwararar bakin haure ke dada kamari a nahiyar Turai.

Des réfugiés à leur arrivée à la gare de Keleti, à Budapest, en Hongrie, le 2 septembre 2015.
Des réfugiés à leur arrivée à la gare de Keleti, à Budapest, en Hongrie, le 2 septembre 2015. REUTERS/Bernadett Szabo
Talla

Kasar Austriya zata dauki nauyin sauke yan gudun hijirar kasar Syriya dubu 10, a yayin da Jamus zata tarbi 5’zuwa dubu 7 da suka isa kasar a cikin Motocin Safa, da Jiragen kasa. Biritaniya itama bayyana aniyarta na daukar nauyin yan gudun hijirar na Syriya dubu 15.

A birnin Athènes na kasar Girka kuma, wani Jinjiri ne da iyayansa suka yo hijira da shi, daga tsibirin 'Agathonissi ya rasa ransa, sai dai har zuwa wannan lokaci mahukumtan kasar ta Girka basu bayyana dalilin mutuwar tasa ba.

A kalla bakin haure 500 ne yanzu haka da suka makale a kasar Hongri, tsawon kwanaki, ke ci gaba da dakar sayyada daga babbar tashar birnin Budapest babban birnin kasar ta Hongri, zuwa kan iyakar kasar da Austriya tafiyar daka kiyasta cewa ta kai ta kilo mita 175
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.