Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya za ta magance kwarrarar bakin haure

A jiya Litinin Gwamnatin kasar Britaniya tayi alkawarin samarda sabbin matakan yaki da bakin haure dake shiga kasar.Wannan na zuwa ne a dai dai lolacin da labarun bakin hauren da suka shiga kasar daga mashigar Calais a Faransa ke daukar hankulan jama’a. 

Wasu bakin haure a yankin Calais dake kasar Faransa
Wasu bakin haure a yankin Calais dake kasar Faransa REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Mahukuntan sun ce daga yanzu za a rinka hukunta masu gidajen haya da basu kori wadanda suka shiga kasar ta barauniyar Hanya ba, inda za a yiwa wadanda suka take dokar, daurin da ya kai na shekaru 5 a gidan yari.
Matakin, da Sakataren al’ummomi Greg Clark ya sanar, zai zama daya daga cikin abubuwan da majalisar Dokokin kasar ta Birtaniya zata yi muhawara a kai, cikin ‘yan watanni masu zuwa.
Batun bakin haure na daya daga cikin lamura masu daukar hankula a siyasar kasar Birtaniya, kuma Gwamnatin Firaminista David Cameron ta shafe shekaru tana kokarin rage yawan bakin dake shiga kasar.
A makon da ya gabata Birtaniya tayi alkawarin kudi EURO miliyan 10, don bunkasa katangar dake a hanyoyin karkashin kasa a yankin Calais, da kuma samar da ci gaban ayyukan shige da fice, da suka hada da samar da karnuka masu bincike.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.