Isa ga babban shafi
Birtaniya

Ana kwana a kwale-kwale saboda tsadar haya a London

Saboda tsadar kudaden hayar gidaje ya sanya wasu mazauna birnin London a Birtaniya na bin hanyoyin samun wuraren kwana masu sauki. Rahotanni sun wasu na kwana cikin kwale kwale a cikin ruwa.

Titin Oxford a Birnin London
Titin Oxford a Birnin London David Crespo/ Getty images
Talla

Kwana a cikin kwale kwale ko kananan riragen ruwa na bai wa mutane da dama sha’awa, musamman in aka buba yadda hakan ke taimakawa wajen kaucewa tsadar kudin haya, ga mai amfani da shi.

Jim Bryden, dan shekaru 39 da ke aikin koyarwa, na rayuwarsa ne a kwale kwale tare da budurwarsa, da karensu, ya ce kwai wadanda ba su da zabi face su koma kwana cikin kwale kwalen, sakamakon wa’adin makonni biyu da aka ba shi ya fice daga inda ya ke saboda rashin kudi.

Mikaela Khan-Parrack, mai shekaru 26, da ya shafe shekaru 4 yana kwan kan ruwa, ya ce in mutum bai san harkar cinikin kwale kwale ba, yana iya sayen wadanda zai yi ta ba shi matsala.

Duk wannan dai na faruwa ne sakamakon yadda kudin haya ya karu zuwa kusann rabin albashin mai matsakaicin karfi a Birtaniya.

Lamarin ya sa ma su bayar da hayar kwale kwalen ke barje guminsu, duk kuwa da cewa harkar ta saba ka’ida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.