Isa ga babban shafi
Birtaniya

Zanga-zangar adawa da siyasar tsuke aljihun gwamnatin Birtaniya

A birnin London na kasar Birtaniya dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da siyasar tsuke bakin aljihi da Firaminista David Cameroun ke kan aiwatarwa.

Titin Oxford Street, a birnin London
Titin Oxford Street, a birnin London David Crespo/ Getty images
Talla

Wannan dai ita ce zanga-zangar farko domin nuna adawa da gwamnatin Cameroun tun bayan zaben majalisar dokokin kasar da aka yi a ranar 7 ga watan mayun da ya gabata.

Masu zanga-zangar a karkashin inuwar kungiyoyi kamar People’s Assembly, sun fara tattakin ne daga harabar babban bankin Ingila da ke London sannan suka dunguma zuwa tsakiyar gari inda ake da manyan cibiyoyin gwamnati da kuma sauran cibiyoyin hada-hada, inda suka bayyana cewa ba za su amince da shirin gwamnatin ta Cameroun ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.