Isa ga babban shafi
Rasha

Dakarun Rasha na gudanar da atisayen tunkarar harin bazata.

Hukumomin kasar Rasha sun umarci dakarun sojan sama kasar, da su fara wani kwara kwaran atisayen shirin tunkarar duk wani harin da za’a iya kai wa kasar.Wannan dai ya biyo bayan zaman dar dar daakae yi ne tsakanin kasar da kasar Ukraine.

Dakarun kasar Ukraine dake sintiri a iyakar ta da Rasha.
Dakarun kasar Ukraine dake sintiri a iyakar ta da Rasha. Reuters/路透社
Talla

A wata sanarwar da rundunonin sojan kasar suka fitar, tace dakarun na Rasha sun gudanar da atisayen ne a wani sansanin soja dake kudancin kasar.

Atisayen zai duba yadda dakarun na Rasha zasu iya tunkarar duk wani harin da za a iya kai wa kasar, inda za’a ayi amfani da kuramen jiragen sama, don daukara hotunan yadda suke tunkarar hare haren na gwaji.

Dama dai shugaba Vladimir Putin yayi ta bayar da umarnin gudanar da irin wadannan atisayen cikin ‘yan watanin da suka gabata, duk kuwa da yadda kasashen duniya suke Allah wadai da matakin.

Cikin ‘yan watannin nan, jami’an gwamnatin kasar ta Rasha sun mayar da hankali wajen sake fasalin rundunonin sojan kasar, musamman ta bangaren kayan aiki irin na zamani, da horas da dakarun kasar.

Sai dai kungiyar Tarayyar Turai, da kungiyar tsaro ta NATO suna ci gaba da diga ayar tambaya kan dalilin wadannan sabbin tsare tsaren, dake zuwa a daidai lokacin da ake zaman dar dar, sakamakon zargin da ake wa hukumomin birnin Moscow, da baiwa ‘yan tawayen gabashin Ukraine goyon baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.