Isa ga babban shafi
Ukraine

Amurka ta tura kwararru domin ba dakarun Ukraine horo

Kimanin Jami’an Sojin Amurka 300 sun isa Ukraine domin ba dakarun kasar horo wadanda ke yaki da ‘Yan tawaye da suka mamaye gabacin Ukraine. Tawagar Jami’an na Amurka sun isa yammacin Ukraine ne tun a ranar Talata zuwa Laraba, inda za su shafe watanni shida suna ba bataliyar dakarun Ukraine horo na musamman domin yaki da ‘Yan tawaye da ke samun goyon bayan Rasha.

Sojojin Ukraine da ke fada da 'Yan tawaye.
Sojojin Ukraine da ke fada da 'Yan tawaye. AFP PHOTO / ANTOLII STEPANOV
Talla

Kasashen yammaci dai na zargin Rasha akan ita ke ba ‘Yan tawaye makamai, zargin da kuma Rasha ke musantawa.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 6,000 suka mutu a rikicin Ukraine.

Masu sharhi dai na ganin Amurka ta yi haka ne domin fusata Rasha da ke zarginta da hura wutar zanga-zangar da ta yi sanadin kawo karshen gwamnatin Viktor Yanukovich mai ra’ayin Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.