Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

NATO na son a ba wakilan OSCE damar shiga gabacin Ukraine

Kungiyar tsaro ta NATO/OTAN ta yi kira ga Rasha ta dakatar da ba ‘Yan tawayen Ukraine goyon baya tare da yin kira a ba wakilan kungiyar OSCE da ke sa ido ga sha’anin tsaro a Turai damar shiga yankin gabacin Ukraine domin tabbatar da an janye makamai a yankin.

Manyan makaman 'Yan tawaye a gabacin Ukraine
Manyan makaman 'Yan tawaye a gabacin Ukraine REUTERS/Marko Djurica
Talla

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce akwai bukatar a ba wakilan kungiyar OSCE damar shiga gabacin Ukraine domin tabbatar da an janye makamai a karkashin yarjejeniyar da Ukraine da ‘Yan tawaye suka amince a birnin Minsk na Belarus.

Duk da an fara janye makaman, amma NATO ta ce akwai bukatar tabbatar da an janye makamai baki daya tare da sanin inda aka dosa da su.

NATO na bukatar a ba wakilan kungiyar OSCE da ke sa ido ga sha’anin tsaro a Turai damar shiga yankin gabacin Ukraine domin ganewa idonsu yadda ake mutunta yarjejeniyar da aka kulla a Minsk.

Kungiyar NATO ta yi kira ga Rasha ta janye dakarunta a Ukraine tare da dakatar da nuna goyon bayan da ta ke ba ‘Yan tawayen kasar da suka karbe ikon gabacin Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.