'Yan Sandan Faransa sun bincike Salhi da ya kai hari a Kasar
Jami’an ‘yan sandan Faransa sun binciki mutumin nan da ake zargi da kaddamar da hari a wata cibiyar ajiyan iskar gas a ranar jumma’ar data gabata a Faransa.
Wallafawa ranar:
Mutumin mai suna Yasin Salhi mai shekaru 35, ya fille kan wani tare da raunata wasu da dama bayan ya jefa abubuwa masu fashewa a harin
Majiyar yan sandan ta bayyana cewa an binciki Salhi inda aka gano cewa ya aika wa wani hotan kan da ya fille ta shafin Whatsup, Kuma ana zatan lambar da ta karbi sakon ta kasar Canada ce.
A cewar ‘yan sandan suna ci gaba da kokarin gano ainihin wanda Salhi ya tura wa sakon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu