Isa ga babban shafi
Faransa

An kai mummunan hari a Faransa

Kasashen duniya na ci gaba da aike wa Faransa da sakon alhini tare da yin allawadai da mummunan harin da wani dan Ta’adda ya kai a yau Juma’a a wata cibiyar gas a Lyon.  Tuni ‘Yan Sanda suka cafke maharin wanda ya fille kan wani tare da raunana wasu da dama bayan ya jefa abubuwa masu fashewa a cikin cibiyar ta gas mallakin Amurka.

‘Yan Sanda sun cafke maharin wanda ya fille kan wani tare da raunana wasu da dama bayan ya jefa abubuwa masu fashewa a cikin cibiyar ta gas mallakin Amurka.
‘Yan Sanda sun cafke maharin wanda ya fille kan wani tare da raunana wasu da dama bayan ya jefa abubuwa masu fashewa a cikin cibiyar ta gas mallakin Amurka. AFP PHOTO/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Da misalin karfe 10 na safe ne wani mutum ya kai harin. An ga maharin dauke da Tuta mai kama da ta Mayakan IS da ke da’awar jihadi a gabas ta tsakiya.

Maharin ya jefa wasu abubuwa masu fashewa a lokacin da ya kai harin inda ya raunana mutane da dama tare da kashe mutum guda wanda aka tsinci kansa da aka fille a harabar cibiyar.

Yanzu haka ‘Yan sanda na tsare da Yassin Salhi wanda ake zargi ya kai harin tare da wani da ke sintiri a harabar cibiyar gas din a lokacin aka kai harin.

‘Yan sanda kuma sun cafke matar maharin.

Amurka da kasashen Turai da suka hada da Spain da Jamus da Birtaniya sun yi allawadai da harin tare da aikewa Faransa da sakon alhininsu.

Shugaba Hollande wanda ya fice taron shugabannin kasashen Turai a Brussels ya dangata harin a matsayin ta’addanci tare da jajantawa wadanda harin ya rutsa da su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.