Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta sake farfado da kamfanin Areva

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce, gwamnatinsa Za ta sake farfado da kamfanin samar da makamashin nukliyar kasar Areva da ke cikin damuwa, a yayin da katafaren kamfanin samar da makamashin kasar EDF zai kasance mafi karfin jari a tafiyar da ayukan injinan samar da nukliyar nukliyar kamfanin na Areva. Shugaban ya fadi hakan ne a wani zaman taron da ya jagoranta tare da manyan ministocinsa a fadarsa da ke birnin Paris.

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande REUTERS/Enrique de la Osa
Talla

Wani babban jami’i na kusa da shugaban kasar ta Faransa Francois Hollande yace kalubalen da ke kan kamfanin Areva, bai tsaya a kan matsalolin kudin da kamfanin na Areva ke fuskanta ba, har ma da batun sake fasalta gaba dayan kamfanin, domin sake dora shi kan sabuwar tirbar ci gaba.

Kafin gudanar da zaman taron Kakakin gwamnatin France Stéphane Le Foll, ya ce, a cikin watan Yuli mai zuwa ne, za a gabatar da shawarwarin da zasu sake fasalta kamfanin.

Bayan Fuskantar mummunar faduwa ta kimanin biliyan 5 na Euro a shekarar 2014, a halin da ake ciki a yau Areva na bukatar kimanin kudi Euro biliyan 6 zuwa 7 domin sake farfado da kumarin baitul malinsa daya rame.

Matakin da babu tantama zai yi awon gaba da kimanin guraban aiki dubu 6 na ma’aikatansa, kuma dubu 3 zuwa 4 na a cikin kasar ta Fransa ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.