Isa ga babban shafi
Faransa

Kamfanin Areva zai kori ma’aikatansa 6,000

Kamfanin Areva na Faransa da ke aikin hako ma’adinin Uranium ya sanar da matakin korar ma’aikatansa 6,000 a sassan kasashen duniya, a wani mataki na datse yawan kudaden da kamfanin ke kashewa. Daraktan kula da hidimar ma’aikatan kamfanin Francois Nogue ya ce za su kori ma’aikata tsakanin 5,000 zuwa 6,000 a bana.

Shugaban Areva Luc Oursel
Shugaban Areva Luc Oursel REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Ma’aikata kusan 3,000 zuwa 4,000 matakin zai shafa a kasar Faransa.

Tuni kamfanin Areva ya bayyana kudirin datse yawan kudaden da ya ke kashewa da kusan kashi 15 a Faransa tare da datse kashi 18 a sassansa da ke sauran kasashen duniya.

A bara, kamfanin Areva ya yi hasarar kudi yuro Biliyan 4.8, lamarin da ya sa kamfanin ya fito da wani tsarin ajiye kudadensa kusan Biliyan guda nan da wasu shekaru masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.