Nijar
Nijar ta cim ma yarjejeniya da Areva
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun cim ma yarjejeniya da kamfanin hako Uranium na Areva bayan share tsawon watanni 18 ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu. Wannan tattaunawa ta dauki dogon lokaci sakamakon yadda gwamnatin kasar Nijar ta kara wa kamfanin kudaden haraji, tare da nema ya gudanar da wasu ayyukan ci gaban jama’ar yankunan da ya ke gudanar da ayyukansa.
Wallafawa ranar:
Talla
Kamfanin Areva ya amince da karin kudaden haraji karkashin yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin Nijar. Wannan kuma ya shafi ciboyoyin Kamfanin a Somair da Cominak.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu