Isa ga babban shafi
Croatia

An yi bikin tuna fursononin ‘Yan Nazi a Croatia

Al’ummar kasar Croatia sun gudanar da bikin tuna dubban mutanen da ‘Yan Nazi suka kashe a zamanin yakin duniya na biyu a sansanin da aka karya ‘Yan Nazin shekaru 70 da suka gabata. 

Wasu daga cikin masu zanga-zanga  a birni Zagreb
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a birni Zagreb Reuters/Davor Kovacevic
Talla

Croatia ta yi jimamin kisan daruruwan sabiyawa da Yahudawa da ‘yan Nazi suka kashe a kasar a yayin da aka cika shekaru 70 da karya ‘yan Nazi a jiya Lahadi.

Daruruwan mutane ne suka halarci sansanin Jesenovac da suka hada da shugabannin addini da jami’an gwamnati da kuma wadanda suka tsira daga hare haren na ‘yan Nazi.

A jawabin da ya gabatarwa ‘yan kasa Firaministan Croatia Zoran Milanovic yace kasarsu da ta samu ‘yanci a 1991 ta nisanta kanta da kundin tsarin mulkin ‘yan nazi da suka kafa sansanin Jesenovac a 1941.

An gudanar da bikin ne dai a yayin da ake cika shekaru 70, da fursononi kimanin 600 suka yi kokarin tserewa daga sansanin ‘yan Nazi, amma cikinsu 90 ne kawai suka tsira.

Kuma tun daga lokacin ake gudanar da bikin jimamin mutuwar mutanen a Croatia da Poland duk shekara domin karramar mutanen da suka mutu.

Adadin dai mutane 80,000 aka ruwaito sun mutu a hannun ‘yan Nazi a lokacin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.