Isa ga babban shafi
Faransa

An shigar da karar kafafan yada labarai Kotu saboda harin Faransa

Wasu mutane 6 sun shigar da karar kafafan yada labarai na Kasar Faransa Kotu, sakamakon zarginsu da laifin haska hotan bidiyon su a lokacin da ‘yan bindiga suka kaddamar da hari a kamfanin mujallar Charlie Hebdo

Jami'in Dan Sanda a gaban Kamfanin Mujallar Charlie Hebdo
Jami'in Dan Sanda a gaban Kamfanin Mujallar Charlie Hebdo REUTERS/Regis Duvignau/Files
Talla

Kafafan yada labaran sun dau hotan bidiyon mutanen bayan sun buya a dakin na’urar sanyaya abinci ta Kantin Kosher dan gudun salwantar rayukansu a harin da ‘yan bindigan suka kai a kamfanin barkonci na Mujallar Cahrlie Hebdo a watan Janairun wannan shekarar.

Mutanen sun zargi kafafan yada labaran da nuna wa duniya inda suka buya kai tsaye, yayin da suka ce, hakan nada hatsarin gaske, lura da cewa, a dai dai lokacin ne, daya daga cikin ‘yan bindigan mai suna Amedy Coulibaly ya kutso kai cikin kantin, inda nan take ya bude wuta tare da kashe mutane 4 a Kantin.

Idan har an sami kafofin yada labaran da laifi, ana iya zantar masu da hukuncin dauri na tsawon shekara guda ko taran kudi Euro dubu 15.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.