Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

An yi taron adu'a ga wadanda suka mutu a hadarin jirgin saman Germanwing a Faransa

Yau assabar aka gudanar adu’oin neman gafara ga fasinjoji nan 150 da suka rasa rayukansu a cikin hatsarin jirgin saman Germanwing na kasar Jamus.An gudanar da addu’o’in ne a majami’ar Notre-Dame-du-bourg dake yankin Digne-les-Bains kudu maso gabashin kasar Fransa, dab da tsaunukan da hatsarin ya faruDaya daga cikin wadanda suka halarci adu’o’in, Marie Pierre ta bayyana cewa ta halarci wurin ne domin neman gafarar ubangiji ga wadanda suka rasa rayukansu, kuma a cewar ta, abin ne mai muhimmanci a gudanar da irin wadannan adu’o’i a tafarkin addini.Ita ma wata tsohuwa ‘yan shekaru 81 1 dunuya mai suna Jacqueline, ta bayyana kaduwarta kan wannan hatsarin inda tace ya kamata a tallafawa iyalan mammatan, da kuma su kansu da suka rigamu da addu’o’in neman gafarar ubangiji.Mafi yawancin wadanda suka halarci addu’o’in tsofaffi ne dake tafiya tare da taimakon sanda, amma duk da haka sun nuna alhini da kuma zumuncin dake tsakaninsu da iyalai da kuma wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin.Baya ga furanni da mahalarta adu’ar suka jera a wajen, sun kuma kunna kyandra 150, wadanda sune adadin yawan mamatan.Shagulgulan aduu’in dai sun samu halartar Bishop din yankin Digne Mr. Jean-Philippe Nault, dan shekaru 49, wanda ya kasance bishop mafi karancin shekariu a kasar Faransa. 

Wasu da suke jajanta mutuwar hadarin jirgin saman Germanwing
Wasu da suke jajanta mutuwar hadarin jirgin saman Germanwing AFP PHOTO / BORIS HORVAT
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.