Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya ziyarci Hollande

A karon farko tun bayan da ya sauka daga karagar mulki, a yau alhamis tsohon shugaban Faransa Nicola Sarkozy ya ziyarci fadar shugaban kasar domin ganawa da Francois Hollande, inda kuma suka tattauna halin da Faransa ke ciki sakamakon  hare-haren 'Yan bindiga da suka addabi kasar.

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy tare da Shugaba  François Hollande, ziyarar da ya kai fadar shugaban kasar kan batun harin  Charlie Hebdo.
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy tare da Shugaba François Hollande, ziyarar da ya kai fadar shugaban kasar kan batun harin Charlie Hebdo. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Sarkozy ya ce jam’iyyarsa na goyon bayan dukkanin matakan da gwamnatin kasar za ta domin yaki da ta’addanci.

A ranar Laraba ne wasu mahara suka kashe mutane 12 a ginin mujallar Charlie Hebdo da ta ci zarafin musulmi.

Sarkozy yace ba za su taba ja da baya baa game da manufofin Faransa ba, a cewarsa za su ci gaba rayuwa kamar yadda Faransa suke kuma ba wanda ya isa ya hana.

Sarkozy yace halin da Faransa ke ciki na jmami, lokaci ne da ake bukatar samun hadin-kai a tsakanin Faransawa, domin nuna kyama ga ta’addanci da kuma masu aikata kisa.

Sarkozy yace jami’iyyarsa na goyon bayan dukkanin matakan da za a dauka dangane dayaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.