Isa ga babban shafi
Faransa

Kasashen Turai suna fuskantar barazana

Kasashen yammacin Turai na fuskantar babbar barazana daga ‘Yan bindiga masu da’awar Jihadi bayan harin da wasu suka kaddamar a kan Mujallar Charlie Hebdo, da ta ci zarafin Musulmi. Barazanar ta fi girma a Kasashen Turai da suka kaddamar da yaki da ta’ddanci.

Faransawa suna jimamin harin Charlie Hebdo a harabar Muja'mi'ar Notre Dame a Paris
Faransawa suna jimamin harin Charlie Hebdo a harabar Muja'mi'ar Notre Dame a Paris REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Masana na ganin kasashen yammacin Turai za su fuskanci barazanar hare hare bayan harin da ‘yan bindiga suka kai wa Mujallar Charlie a Faransa wacce ta yi wani zanen da ta danganta da Manzon Allah SAW.

Mahakuntan Paris a Faransa sun tabbatar da mutuwar mutane 12 a harin da ‘yan bindigar suka kaddamar dauke da AK47.

Zuwa yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin amma masana suna ganin harin alamu ne da ke nuna kungiyoyin mayaka irinsu Al Qaeda da Taliban da IS za su kaddamar da hari ga kasashen yammaci.

Faransa tana cikin kasashen da suka hada hannu da Amurka wajen kaddamar da yaki akan Mayakan IS da ke da’awar Shari’a a Iraqi da Syria.

Tuni jami’an leken asirin Turai suka bayyana fargaba akan yawan Turawan da ke shiga ayyukan Mayakan IS a kasashen Iraqi da Syria.

Zanen Mujallar dai ya janyo bore a kasashen musulmi tun lokacin da ta wallafa zanen cin mutuncin addinin Musulunci a 2006.

A watan Nuwamban 2011 an taba kai wa Jaridar harin bom.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.