Isa ga babban shafi
Faransa

Jami’an tsaro sun dukufa don gano maharan Charlie Hebdo

Jami’an tsaron a kasar Faransa sun kaddamar da gagarumin samame dan bankado wasu yan uwan juna biyu da ake zargi da kashe mutane 12 a mujallar Charlie Hebdo

REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Rahotanni daga kasar ta Faransa na cewar maharan da suka kai 3 rufe da fuskokinsu, sun dirarwa Kamfanin mujallar ne a lokacin da ake wani dan kwarya-kwaryan taron tantance bayannai, bayan da Mijallar ta yi wani zane da ya ci mutuncin Annabi Muhammadu, kamar yanda ta taba yi a baya.

Sai dai bayan kai wannan harin, mutane sama da 100,000 suka yi gangami dan nuna alhininsu da harin, yayin da shugaba Francois Hollande kuma, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga ranar Alhamis, da kuma alkawarin mayar da martanin da ya dace kan maharan.

A wani labarin kuma Majalisar dinkin Duniya da Sarauniyar Ingila da Fafaroma Francis sun bi sahun shugabanin kasahsen duniya wajen Allah wadai da mummunar harin da wasu yan Bindiga suka kai Paris inda suka hallaka mutane 12 a mujallar ta Charlie Hebdo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.