Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

An gudanar da zaben raba gardama a yankin Cremea

Dubun dubatar mazauna lardin Cremea mallakin kasar Ukraine ne suka fito a wannan lahadi inda suka jefa kuri’unsu domin bayyana aniyarsu ta ko dai hadewar yankin da kasar Rasha ko kuma samun ‘yancin-kai daga kasar Ukraine.

Rumfar zabe a Simferopol na kasar Ukriane
Rumfar zabe a Simferopol na kasar Ukriane REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

Duk da cewa ba a kai ga fitar da sakamakon zaben ba, to amma bisa ga dukkan alamu masu goyon bayan hadewa da kasar Rasha ne za su yi galaba a zaben.
A wata rumfunar zabe da ke garin Sebasttopol, inda ake da dimbin masu ra’ayin Rasha, daga cikin kuri’u 65 da aka jefa, duka duka kuri’a daya ce ke adawa da hadewa da Rasha.

A wannan litinin ministocin harkokin wajen kasashen Turai za su gudanar taro domin sanar da daukar matakai a kan kasar Rasha sakamakon rawar da take takawa a wannan kuri’a ta raba gardama.

Shugabar gwamnatin Jamus kuwa Angela Merkel, wadda ke tattauwa ta wayar tarko da shugaba Vladimir Putin, ta bayyana goyon bayanta ga shirin aikewa da karin masu sanya ido na Kungiyar Tsaro da kuma Hulda a tsakanin Kasashen Turai ta OSCE zuwa gabashin Ukraine.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.