Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

An fara zaben raba gardama a yankin Crimea na Ukraine

Dazun nana ka bude rumfunan zabe a yankin Crimea, a zaben raba gardaman da aka fara kan ko yankin ya koma karkashin ikon kasar Rasha ko ci gaba da zama a Ukraine da karin iko. An ga wani mutum ya shiga rumfar zabe a Simferopol, yayin da wakilan kamfanin dillacin labarum Faranasa na AFP suka ga wasu mutanen kimanin kimanin 20, sun fito don yin zabe a garin Bakhchysaray, da akasarin ‘yan kabilar Tatar musulmi suke zaune a yankin na Crimea.Dama shugabannin musulmin kasar sun nemi a kauracewa zaben raba gardaman.Kusan mutane miliyon 1 da rabi ake sa ran za su kada kuri’a, kan makomar yankin, da akasarin mazaunan shi ‘yan asalin kasar Rasha ne.Mazaunan suna da zabin komawa karkashin Rasha, ko kuma samun karin fada a ji, da zama a Ukraine.Cecekucen da kasashen yammacin duniya ke yi kan yankin, ya sa aka koma rikici irin na zamanin yakin cacar baki, inda harkokin diplomasiyya tsakanin kasashen ke tangal tangal. 

Wasu masu zanga zangar adawa da Rasha a Ukraine
Wasu masu zanga zangar adawa da Rasha a Ukraine REUTERS/Mike Theiler
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.