Isa ga babban shafi
Ukraine

Ukraine: Rasha da Amurka zasu tattauna akan Crimea

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya isa birnin London a yau Juma’a domin tattaunawa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov game da makomar yankin Crimea da ke shirin kada kuri’ar amincewa su koma ikon Rasha a ranar Lahadi.

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry yana magana a kusa da Firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk a Washington
Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry yana magana a kusa da Firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk a Washington REUTERS/Gary Cameron
Talla

Amurka tana neman a dakatar da zaben jin ra’ayin Jama’a da shugabannin yankin Crimea suka shirya masu ra’ayin Rasha.

Ana sa ran John Kerry zai gargadi Sergei Lavrov akan aiwatar da zaben jin ra’ayin Jama’a zai sa Amurka da kasashen Turai su dauki matakin Takunkumi akan Rasha.

Kafin ya isa London John Kerry yace sabanin da ke tsakanin Rasha da Amruka dangane da kasar Ukraine na barazanar ruguza kyakkyawar huldar da ke tsakanin kasashen biyu kan rikicin kasar Syria, wajen kokarin raba gwamnatin Bashar Al’asad da makamai masu guba.

Mafi yawancin mutanen Crimea suna magana ne da harshen Rashanci kuma jekadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya yace suna da ‘yancin zabi akan Rasha ko Ukraine.

Amma Shugaban kabilar Tatar a yankin Crimea a kasar Ukraine, wadanda mafi yawancinsu ke magana da harshen Turkiya, ya yi kira ga al’ummar yankin su kauracewa zaben raba gardama da za’a yi a ranar Lahadi domin komawa ikon kasar Rasha.

Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya soki Rasha da nufin kare al’ummar Tatar masu magana da harshen Turkiya.

Rahotanni sun ce  Erdogan ya zanta da Shugaba Putin na Rasha ta wayar Tarho yana mai shaida masa cewa Turkiya tana cikin damuwa game da makomar ‘yan kabilar Tatar a yankin Crimea.

Kodayake mafi yawancin mutanen Crimea, suna magana ne da Rashanci amma akwai alaka tsakanin al’ummar Tatar da Turkiya, tun a zamanin daular Ottoman wadanda suka kunshi kashi 12 na mutanen Crimea.

A ranar Lahadi ne mutanen Crimea za su kada kuri’ar amincewa su koma Rasha ko ci gaba da zama a Ukraine, yayin da kasashen yammaci ke ci gaba da caccakar Rasha da suka ce tana amfani da karfi don mamaye yankin.

Tuni bangaren gwamnatin Ukraine suka yi watsi da zaben raba gardamar wanda suka ce baya cikin tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.