Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka

Amurka zata taimakawa Ukraine

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, wanda ya zanta da manema labarai jim kadan bayan ya gana da Firaministan Ukraine Arseni Yetsenyuk yace kutsen da Rasha ta yi a yankin Crimea mallakin Ukraine, abu ne da ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Shugaban Amurka Barack Obama yana ganawa da Firaministan Ukraine Arseni Yatseniuk
Shugaban Amurka Barack Obama yana ganawa da Firaministan Ukraine Arseni Yatseniuk REUTERS/Larry Downing
Talla

Obama yace Amurka za ta ci gaba da marawa Ukraine baya domin tabbatar da cewa ba wani yankin da ya balle daga cikinta, tare da yin kira ga shugaba Vladimir Putin akan ya canza salo kan yadda ya ke tafiyar da wannan batu, tare da yin gargadin daukar matakai a kan Rasha.

Akwai gargadi kuma da shugabannin Kasashen 7 masu karfin tattalin arziki suka yi wa kasar Rasha akan ta kaucewa mamaye Yankin Crimea da ke kasar Ukraine, a dai dai lokacin da Yankin ke shirin gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a dan ballewa daga kasar.

Wannan gargadin na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaba Barack Obama ke ganawa da Firaministan riko Arseniy Yatsenyuk, inda suka tattauna kan halin da kasar take ciki, da kuma yadda Amurka zata taimakawa Ukraine.

Firaministan rikon yace ba zasu yi amfani da karin soji ba wajen kwato Yankin na Crimea ba, ganin yadda sojojin Rasha suka mamaye na su a Yankin.

A bangare daya kuma jami’an Yankin na Crimea na ci gaba da shirin zaben raba gardaman, wanda zai bai wa al’ummar Yankin bayyana ra’ayinsu na hadewa da kasar Rasha ko ci gaba da zama a Ukraine.

Tuni dai Majalisar Yankin ta ayyana matsayinta na hadewa da Rasha, matakin da ya samu suka daga sassa dabam dabam na nahiyar Turai.

shugabanin kasashen Turai zasu gudanar da wani taro a makon gobe don bayyana takunkumin da zasu sanyawa Rasha muddin aka kasa warware matsalar Ukraine ta hanyar diflomasiya.

Kafin dai taron, ministocin tsaro da harkokin wajen Faransa, zasu ziyarci Moscow don ganawa da takwarorinsu kan matsalar.

Rikicin Ukraine ya barke ne tun lokacin da hambararren shugaban kasa Vicktor Yanukovych ya kulla yarjejeniyar kasuwanci da Rasha sabanin Kungiyar Turai, lamarin da ya sa ‘Yan adawa masu ra’ayin Turai suka bazama saman tituna suna gudanar da zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.