Isa ga babban shafi
Ukraine

An shirya yin zanga-zangar karo da juna a Ukraine

Magoya bayan shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych sun shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zanga domin karo da ‘Yan adawa da ke kiran sai shugaban ya yi murabus a birnin Kiev. Duk da barazanar da Amurka ta yi na kakabawa shugabannin kasar tukunkumi amma har yanzu ba a samu kwanciyar hankali ba a kasar Ukraine.

Daruruwan masu zanga-zanga a kasar Ukraine
Daruruwan masu zanga-zanga a kasar Ukraine REUTERS/Alexander Demianchuk
Talla

Daruruwan masu adawa sun kwashe makwanni uku suna zanga-zangar kin jinin gwamnatin Yanukovych saboda ya ki amincewa da kawancen Ukraine da kungiyar Tarayyar Turai.

Amma domin hura wutar rikicin kasar, magoya bayan shugaban sun shirya gudanar da zanga-zanga domin karo da ‘Yan adawa.

Tuni dai Amurka tace tana sa ido akan abin da ke faruwa a Ukraine tare da kira ga mahukuntan kasar su dauki matakan da suka dace domin samun jituwa da ‘Yan adawa bayan an samu arangama tsakanin ‘Yan sanda da masu zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.