Isa ga babban shafi
Ukraine

Amurka ta yi barazanar sanya wa Ukraine Takunkumi

Kasar Amurka ta yi gargadin cewa matukar hukumomin kasar Ukraine suka ci gaba da yin amfani da karfi akan masu zanga-zanga, to hakan zai sa ta dauki matakin kakabawa kasar takunkumin hana tafiya akan shugabannin kasar da kuma rike wasu kudade da kadarorin kasar da ke Amurka.

Jami'an tsaro suna arangama da daruruwan Masu zanga-zanga a kasar Ukraine
Jami'an tsaro suna arangama da daruruwan Masu zanga-zanga a kasar Ukraine REUTERS/Valentyn Ogirenko
Talla

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, a yammacin jiya Laraba ya zanta ta wayar tarho da takwaran aikinsa na Ukraine Pavel Lebedev, inda ya sanar da shi cewa Amurka ba za ta lamunce sojoji su shiga a wannan rikici da ake yi tsakanin shugaban mai ci Viktor Yanukovich da ‘yan adawa

Wannan kuma ya biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da masu zanga-zanga inda ‘Yan sanda suka abka dandalin daruruwan mutane da ke gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati.

A jiya Laraba akwai ganawa ta musamman da aka yi tsakanin mataimakiyar sakataren harakokin wajen Amurka Victoria Nuland da Catherine Ashton ta Tarayyar Turai tare da Bangaren shugaba Victor Yanukovych da kuma ‘Yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.