Isa ga babban shafi
Ukraine

‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a Ukraine

‘Yan sandan Ukraine sun yi arangama da masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Kiev babban birnin kasar inda Jam’in tsaro suke kokarin tarwatsa gungun masu zanga-zangar a dandalin da suka mamaye tsawon makwanni biyu.

Kiev, le 11 décembre 2013.
Kiev, le 11 décembre 2013. Reuters
Talla

Rahotanni daga birnin na Kiev, sun ce yanzu haka fiye da mutane dubu goma ne suka taru a wani makeken dandali suke kalubalantar matakin da ‘Yan sanda suka dauka na ruguza rumfunan da suka kafa domin neman shugaban kasar ya yi marabus daga mukaminsa.

A jiya Talata Shugaba Viktor Yanukovych ya gana da wasu tsoffin shugabannin kasar guda uku da shugabar ofishin manufofin ketare ta kungiyar Tarayyar Turai Cathrine Ashton, kan yadda za a kawo karshen tarzomar da ake fama da ita a kasar.

Zanga-zangar kin jinin gwamnatin dai ta barke net un a watan jiya bayan da gwamnatin Viktor Yanukovych ta yi watsi da yarjejeniyar kungiyar Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.