Kungiyar tarayyar Turai da Canada za su saka hanu a huldar kasuwanci
Shugaban kungiyar Tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso gobe zai gana da Firaministan Canada Stephen Harper game da shirinsu na saka hanu a wata yarjejeniya da za ta dauke biyan haraji akan hadahadar kasuwancin bagarorin biyu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugabannin biyu za su gana da ‘yan jarida bayan sun tattauna akan wannan yarjejeniya wacce aka kwashe shekaru huda ana kokarin kammala ta.
“Muna daf da kammala wannan yarjejeniya wacce muka fara kullata tun daga shekarar 2009.” Inji Harper.
Kasar Canada dai na bukatar kungiyar tarayyar turai da su bata damar sayar da namanta a nahiyar tare da rage mata yawan kudaden haraji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu