Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

Kasashen Turai na gudanar da tattaunawa kan Siriya.

Ministocin harakokin wajen kungiyar tarayyar turai sun fara gudanar da wani zaman taronsu a yau juma a a birnin Vilnius na kasar lutueniya domin duba yadda zasu bayar da amsa kan harin makamai masu guba da ake zargin an yi a kasar Syriya.

Majalisar kasashen Turai
Majalisar kasashen Turai learnstuff.com
Talla

Wannan taron nasu na zuwa ne a daidai lokacin da manyan kasashen duniya ke ci gaba da samun baraka kan yiyuwar yin amfani da karfin soja a kan kasar ta Syriya

Ministan kasar Lituaniya Linas Linkevicius ya bayyana zaman taron da cewa na bukatar kara samun fahimta ne tasakanin kasashe mambobin kungiyar ta turai, kafin su san matakin da zasu dauka na bai daya da kuma ake zaton cewar da wuya ba kasar Amurka zasu goyawa baya ba.

Dama dai kasashen Amurka da Faransa na ci gaba da neman hadin kan Duniya domin kaiwa siriya farmakin Soji ta Sama.

Kasar Amurka dai ta Bakin shugaba Obama ta bayyana cewar harin da Amurka ke shirin kaiwa Siriya na dan takaitaccen lokaci ne da bai wuce kwanaki Sittin ba.

Harma akwai bayannan dake nuna cewar Obama ya gana da shugaba Putin na Rasha da manufar gamsar da shi kan batun na harin Siriya, amma suka tashi baram-baram.

Batun kasar Siriya dai ya ya zama babban batu dake daukar Hankali a Duniya bisa yanda kasar Amurka ta kambama shi.

Majalisar kasar Siriya dai ta aikewa Majalisar Amurka cewar karta amince da bukatar Obama, don hakan zai haifar da tashin hankalin Duniya ne kurum.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.