Isa ga babban shafi
Girka

Girka za ta rage yawan kudin da za ta nemi taimako

Ministan ma’aikatar kudin kasar Girka Yannis Stournaras ya ce idan har kasar za ta sake neman wani taimako domin ceto tattalin arzikinta a nan gaba, to zai kasance kwarya-kwaryan taimakon da ba zai wuce na dalar milyan dubu 15. Kasar Girka na a karkashin wani shiri na ceto tattalin arziki ne da asusun lamani na duniya da kuma kungiyar tarayyar Turai, kuma za ta ci gaba da kasancewa a karkashin wannan shiri har zuwa shekara ta 2016.A farkon wannan watan na Augusta, aka bayyana cewa kasashen Turai sun fice daga kangin karayar tattalin arzikin da suka fada tsawon watanni da dama.Ana kuma ganin wannan zai tamaka wa kasashen yankin na Turai su rage bukatar kudaden tallafin da suka yi ta nema a baya. 

Ministan kudin kasar Girka, Yannis Stournaras tare da shugabar hukumar lamani ta Diniya IMF, Christine Lagarde
Ministan kudin kasar Girka, Yannis Stournaras tare da shugabar hukumar lamani ta Diniya IMF, Christine Lagarde REUTERS/Yves Herman
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.