Isa ga babban shafi
EU

Kasashen turai na shirin daukan matakan dakile kwararar bakin haure

Kuniyar Tarayyar Turai ta EU ta nemi a dauki sabbin matakan da za su dakile kwararar bakin haure dake shiga nahiyar domin neman mafaka daga wahalhalun dake addabar kasashensu.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai,  José Manuel Barroso
Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai, José Manuel Barroso REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Kungiyar ta yi wannan kira ne bayan lamarin da ya auku a yankin Lampedusa na kasar Italiya inda daruruwan bakin haure suka mutu a ruwa yayin da suke kokarin shiga nahiyar Turai a wani jirgin ruwa.

Kwamishinan ayyukan cikin gida ta kungiyar, Cecilia Malmstroem wacce ta gana da ministocin cikin gidan kasashen nahiyar turai, ta ce akwai bukatar a kara yawan kudaden da za su ba da damar gudanar da sintiri akan ruwan Meditareniya domin kaucewa aukuwar irin wannan lamari.

“Zan nemi goyon bayan yin hakan domin mu ceto rayukan mutane.” Inji Malmstroem.

Hadarin jirgin na Lampesuda, wanda ya auku a makon da ya gabata ya faru ne a lokacin da wasu ‘yan nahiyar Afrika ke kokarin shiga nahiyar Turai.

A yau Talata ma wasu mutane 400 wadanda suke ikrarin dake ikrarin daga Syria da Falasdinu suke sun isa kasr Italiya inda aka ceto su bayan jirgin ruwansu ya lalace.

A goeb ne ake sa ran Malmstroem za ta ziyarci yankin Lampedusa domin ganewa idonta hadarin day a faru tare Shugaban kungiyar ta EU Jose Manuel Barroso.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.