Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaban Yahudawan Faransa ya yi murabus saboda satar fasaha

Shugaban limaman yahudu a Faransa Gilles Bernheim ya bada sanarwar yin murabus daga mukamin shi bayan ya amsa aikata satar fasaha domin tabbatar da samun ilimin Farfesa a bangaren Falsafa..

Shugaban Yahudawan Faransa Gilles Bernheim da ake kira Rabbi
Shugaban Yahudawan Faransa Gilles Bernheim da ake kira Rabbi AFP PHOTO / POOL / LIONEL BONAVENTURE
Talla

Wannan labarin na Bernheim, ya ja hankalin kafofin yada labaran Faransa kamar yadda Cahuzac ya amsa yana da asusun ajiya a bankunan kasashen waje don kada ya biya haraji.

Bernheim, ya nemi afuwar mabiya da kuma abokanansa da ke kusa da shi a lokacin da ya ke zantawa da gidan rediyon Shalom a Faransa.

A shekarar 2008 ne aka zabi Bernheim a matsayin babban jagoran Yahudawa da ake kira Rabbi, Kuma a shekarun baya wani masanin fasahar intanet ya zargi Bernheim da satar fasahar littafin Jean-François Lyotard a wani littafinsa da ya rubuta game da yahudawa mai taken “Forty Jewish Meditations”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.