Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta fito da dokar yaki da ta'addanci

SHUGABAN kasar Faransa Francious Hollande, ya lashi Takobin fitoda dokar hana ayyukan ta’addanci a kasar, a dai dai lokacin da ‘yan sandan kasar suka kai samamen da yayi sanadin mutuwar mutum 1, aka kuma kama wasu mutum 11 sakamakon wani harin da aka kai a kasar.Franciouse Holland yace kasar Faransa wadda a nahiyar Turai ta kasance kasar da tafi yawan al’ummar Musulmi, ba za ta yi kasa a Guiwa ba wajen kula da bukatun su.Saboda a cewar sa, al’ummar Musulmin kasar Faransa ba magoya bayan ‘yan tawaye bane, suma suna fuskantar kalu-bale daga ‘yan tawayen.Yace za’a cigaba da sa Ido a wuraren Ibada na kasar ta faransa, saboda daya daga cikin kudurin kasar shine tabbatar da kiyayewa da tsaron dukkanin mabiya Addinai.A ranar Assabar ma ‘yan sanda a kasar ta Faransa sun kai samame a wani gida dake cikin birnin Cannes, inda suka binciki wata Mota, bayan kama wasu mutane 2, inji wata kwakkwarar majiya daga cikin jami’ai masu bincike.Uku daga cikin wadanda ake zargin dai an taba samunsu da aikata laifin irinsu safarar miyagun kwayoyi, da Sata, da tada zaune tsaye. 

Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Shugaban kasar Faransa, François Hollande REUTERS/Darrin Zammit Lupi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.