Isa ga babban shafi
Faransa

Daruruwan mutane sun halarci jana’izar daliban Faransa biyu da aka kashe

Daruruwan mutane ne suka halarci jana’izar wasu dalibai biyu 'Yan kasar Faransa da aka kashe da wukake, abinda ya tada hankalin daukacin 'Yan kasar. Kisan daliban, Kevin Noubissi da Sofiane Tadburt, ya sa shugaban kasa, Francois Hollande yayi tattaki zuwa gidajensu, idan ya mika sakon ta’aziyar gwamnati. 

Wajan wata jana'iza a Faransa
Wajan wata jana'iza a Faransa www.jpost
Talla

An dai kama mutane 12 da ake zargi da hannu wajen kisan.

A wani banagre kuma, gwamnatin kasar Faransa, na shirya wata doka da zata sa a hukunta duk wanda aka samu da laifin zuwa kasashen waje dan samun horon tsageranci.

Matakin na zuwa ne watanni shida, bayan kashe mutane bakwai da wani Dan bindiga Mohammed Merah yayi a garin Tolouse.

Shidai Merah yayi ikrarin samun horo a Pakistan da Afghanistan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.