Isa ga babban shafi
Paris- France

'Yan Sanda A Faransa Sun Hana Zanga-Zangan Kyamar Amirka

‘Yan adawa a kasar Faransa  sun soki zanga-zanga da wasu musulmi sukayi a kusa da harabar Ofishin jakadancin Amirka dake Paris.Tsohon Fira Ministan Faransa Francois Fillon na son Shugaban kasar Faransa ya bayyana masu dalilan da suka sa Rundunar ‘yan sanda  suka amince musulmi suyi zanga-zanga a kasar Faransa.Ita ma Shugaban jamiyyar Front National Marine Le Pen ta soki zanga-zangan da musulmi suka yi, inda take cewa nema suke yi su harzuka jama’a.Tsohon Fira Ministan jamiiyar Socialist Jean-Marc Ayrault ya tsaya kai da fata cewa zanga-zangan da musulmi suka gudanar babu izini, kuma ‘yan sanda sunyi aikin su.Bayanai na nuna cewa ‘yan sanda sun fasa taron zanga-zangan inda suka kama mutane 150. 

"Yan Sandan Faransa na hana masu bore zanga-zanga
"Yan Sandan Faransa na hana masu bore zanga-zanga RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.