Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan sandan Faransa sun fara fuskantar tambayoyi game da kisan Merah

Jami’an tsaron kasar Faransa sun fara fuskantar tambayoyi game da kashe mutunin da ya hallaka mutane bakwai da suka hada da yara ‘yan makaranta a jerin hare haren uku daya kai kafin a kashe shi.

'Yan sandan Faransa da suka yi farautar  Mohamed Merah, Toulouse.
'Yan sandan Faransa da suka yi farautar Mohamed Merah, Toulouse. Reuters
Talla

Tuni Shugaba Nicolas Sarkozy ya bayyana cewa tilas a kare faruwar haka a nan gaba, a lokacin da yake ci gaba da yakin neman zaben shi a jiya Alhamis, bayan dakatar da yakin neman zaben na wani lokaci.

Dan takarar shugabancin Faransa na jam’iyyar adawa ta gurguzu, Francois Hollande ya ce abinda ya faru gazawa ce ta fuskar tattara bayanan sirri.

Akwai matsin lamba da manyan Jami’an tsaro ke fuskanta game da yadda suka kashe Muhammed Merah ba tare da tsafke shi a raye ba.

A jiya Alhamis ne ‘Yan sanda suka kashe muhammed Merah a gidan da yake buya a Toulouse bayan kwashe kwanaki biyu suna musayar albarussai.

Wannan ne kuma ya dakatar da yakin neman zaben ‘Yan takarar shugaban kasar Faransa da za’a gudanar da watan Afrilu da Mayu, amma Shugaba Sarkozy ya ci gaba da yakin neman zaben shi a jiya Alhamis inda yace aikin dan bindigar bana gangaci bane.

A wani jawabin na Shugaba Sarkozy da aka nuna a kafar Telebijin, shugaban ya sha alwashin kawo karshen masu tsatstsauran ra’ayi tare da bayyana samar da dokar hukunta mutanen da ke kai ziyara shafin Intanet na ‘Yan ta’adda.

Wannan al’amari na Muhammed Mereh ya girgiza kasar Faransa mai yawan Yahudawa da Musulmi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.