Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin kasar Faransa ta karfafa matakan tsaron kamo maharin da ya hallaka mutane hudu

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya karfafa matakan tsaro a Yankin kudu maso Gabashin kasar, saboda kashe wasu yara Yan makaranta uku da malami daya, a wata makarantar Yahudawa. Ya kuma dakatar da yakin neman zaben sa.Yayin da ya ziyarci makarantar dake birnin Tolouse, Sarkozy ya bayyana cewar, wanna kisan gilla ba wai ya taba Yahudawa bane, ya taba daukacin kasar Faransa ce, kuma yau za’a gudanar da tsayuwa ta minti guda a daukacin makarantun Faransa, dan tunawa da wadanda aka kashe. 

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da jami'an gwamnati yayin ziyarar makarantar Ozar Hatorah a garin Toulouse
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da jami'an gwamnati yayin ziyarar makarantar Ozar Hatorah a garin Toulouse REUTERS/Eric Cabanis
Talla

Kasashen Duniya sun bayyana kaduwarsu da harin da aka kai makarantar Faransa, inda sukayi Allah wadai da harin.

Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana harin a matsayin kisan kai, kamar yadda mai shiga tsakani na Palasdinawa Saeb Erakat ya bayyana shi a matsayin aikin ta’adanci.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ministocin harkokin wajen kasashen Jamus, Birtaniya, Canada, Belgium, Italiya da Australia, duk sun bayyana bacin ransa da kashe yaran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.