Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan Sandan Faransa sun kai samame a mafakar dan bindigar Toulouse

‘Yan Sanda a kasar Faransa, sun kai wani samame a wani gida da suke zargin mafakar dan bindigar da ya hallaka mutane tara a Toulouse. ‘Yan sandan sun ce sun gano adireshin wani dan uwan shi ta kafar intanet tare da gano cewa dan bindigar an taba cafke shi a birnin Kandahar a kasar Afghanistan.

Samamen da 'Yan Sanda suka kai a Toulouse da safiyar Laraba gidan da suke tunanin mafakar dan Bindigar daya hallaka mutane tara.
Samamen da 'Yan Sanda suka kai a Toulouse da safiyar Laraba gidan da suke tunanin mafakar dan Bindigar daya hallaka mutane tara. REUTERS/Pascal Parrot
Talla

Rahotanni sun ce, ‘Yan Sanda biyu sun samu rauni yayin da suka kai samamen don kokarin cafke dan bindigar da ake zargin bafaranshe ne amma dan asalin arewacin Afrika wanda ya yi ikirarin shi dan kungiyar Al Qa’ida ne.

Ministan cikin gidan Faransa Claude Gueant ya shaidawa manema labarai cewa dan bindigar ya zanta da ‘Yan sanda ta kofar shiga gidan inda ya bayyana kansa a matsayin Mujahedeen gwarzon da ke neman daukar fansan kisan da Isra’ila ta yi wa ‘Yayan Falesdinawa.

A hare haren da dan bindigar ya kaddamar, Wadanda suka mutu sun hada da Sojin Faransa uku, da ‘yayan Yahudawa uku da wani malamin Yahudawa.

Mahukuntan Faransa sun bukaci mahaifiyar dan bindigar zantawa da danta tare da neman sasantawa da shi, amma Ministan cikin gidan Faransa yace mahaifiyar bata da wani iko akan dan bindigar.

Tun a ranar 11 ga watan Mayu ne aka fara kai hare hare a birnin Toulouse inda aka kashe Imad Ibn ziaten wani tsohon Soja. Kwanaki hudu kuma aka bindige wasu mutane biyu a birnin Montauban.

Tuni dai shugaba Sarkozy da Hollande suka dakatar da yakin neman zabensu a ranar Litinin saboda hare haren inda ake shirye shiryen gudanar da zabe a ranar 22 ga watan Afrilu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.