Rayuwata
Shirin Rayuwata da ake watsawa daga ranar Litinin zuwa Juma'a na tattaunawa kan batutuwan da suka shafi lamurran mata kamar girki, kwalliya, shafe-shafe, aure, ilimi, matsalar fyade, reno, shayarwa, kula da gida da makamantansu. Shirin na lale marhabin da ra'ayoyin masu sauraro daga kowacce kusuwar ta duniya. Kuna iya tuntubar wannan lambar ta manhajar WhatsApp domin shiga cikin shirin +2349088888990. Wannan shirin na hadin guiwa ne tsakanin Hukumar Raya Kasashe ta Faransa AFD da Sashen Hausa na Radio France International.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
-
Mata sun samu 'yancin zubar da ciki a Faransa
‘Yan Majalisar Dattawan Faransa, sun kada kuri’ar amincewa da sanya ‘yancin zubar da ciki a kundin tsarin mulkin kasar.25/03/202410:00 -
Yadda mata suka gudanar da tashe a watan Ramadan
Tashe al’ada ce da ake gudanarwa a kasar hausa duk shekara, kuma yawanci yara ke yin ta.22/03/202410:00 -
Ra'ayoyi daban-daban na masu sauraren Rfi
Rayuwata,shiri ne da Zainab Ibrahim ke jagoranta, a yau masu saurare kan bayyana ra'ayoyinsu daban-daban daga kowace kusurwa na fadin Duniya.21/03/202410:00 -
Yadda mata suka rungumi aikin karfi a Jamhuriyar Nijar
A yau ya duba yadda yan mata a jamhuriyar Nijar suka dage wajan rungumar ayyukan da a can baya maza kadai ke yinsu, ayyukan da suka hada da kanikanci, gyaran mota, kafinta, da aikin saka wayar wutan lantarki a gida, akwai kuma yasar rijiya, da dai sauransu,20/03/202410:00 -
Muhimmancin karfafawa mata wajen dogaro da kansu
Shirin na wannan rana ya mayar da hankali game da batun yadda masu fafutuka ke neman yadda za a karfafawa mata gwiwar ci gaba da dogaro da kansu ta fannoni da dama.19/03/202410:00 -
An daina bai wa almajirai sadakar abinci a azumi saboda tsadar rayuwa
Shirin Rayuwata na wannan rana ya tattaunawa da wasu almajirai daga jihar Kano ta Najeriya, inda suka bayyana yadda suka daina samun sadakar abinci a cikin wannan wata na azumi, sabanin shekarun baya. Almajiran sun ce ba sa samun abinci a lokacin bude-baki da kuma sahur.18/03/2024 -
Yadda mata suka rungumi sana'ar tukin mota a Jamhuriyar Nijar
Shirin na wannan rana ya mayar da hankali kan yadda mata suka fara shiga harkar tukin mota, sana’ar da ake ganin ta maza ce a baya, abinda ya sa ake ganin tururuwar mata wajen neman lasisin tukin mota15/03/202410:00 -
Yadda ake samun rikici tsakanin uwar miji da matar danta
Takun saka, rashin fahimta ko kuma rikici tsakanin uwar miji da matar ‘da ba sabon abu ba ne tsakanin al’ummar Hausawa, matsalar da kan yi kamari har ta shafi yanayin tasowar zuriya.13/03/202410:00 -
MDD ta horos da matan Nijar kan yadda za su inganta rayuwarsu
A yau shirin rayuwata ya ziyarci Jamhuriyar Nijar, inda Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya IOM da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka kafa wata cibiya a jihar Agades don bai wa mata horo, tare da koya musu ayyukan hannu, baya ga wayar musu da kai dangane da yanayin zamantakewa da ‘yan gari.12/03/202409:58 -
Yadda bikin ranar mata ta duniya ta riski al'umma a Najeriya
A ranar 8 ga watan Maris da ta gabata ne aka gudanar da ranar mata ta duniya, kun kuma ji mabanbantan ra'ayoyi game da yadda ranar ta riski alumma musamman mata.11/03/202410:00 -
MDD ta ce ya kamata a tallafawa mata domin samar da ci gaba ga duniya
Yau take ranar mata ta duniya kamar yadda aka saba gudanar da bikin kowacce ranar 8 ga watan Maris.08/03/202410:00 -
Yadda karancin ilimi ke hana mata kwatar hakkin su a hannun masu cin zarafi
Shirin Rayuwata na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda karancin ilimin shigar da kara ke hana mata samun cikakken adalci daga hukumomi da kungiyoyi, idan an ci zarafin su.06/03/202409:58 -
Yadda iyalai suka shirya gudanar da azumin Ramadana
Shirye-shiryen da iyalai ke ciki na zuwan watan azumin watan Ramadana, daidai lokacin nan da ake fama da tsananin tsadar rayuwa05/03/202410:00 -
Tsadar rayuwa ta jefa iyalai cikin halin kunci a Najeriya
Matsalar tsadar rayuwa na ci gaba da jefa al'ummar Najeriya cikin kunci, duk kuwa da ci gaban da ake samu na farfadowar darajar kudin kasar wato naira.26/02/202410:00 -
Yadda matasan Najeriya ke shan maganin hana haihuwa kafin aure
Shirin Rayuwata na wannan rana ya yi nazari ne kan yadda wasu matasa a Najeriya ke shan magungunan hana haihuwa tun ma kafin aurensu, inda suke cewa, hakan zai ba su damar cin angwanci da amarci na tsawon lokaci.20/02/202410:00
Shirin Rayuwata da ake watsawa daga ranar Litinin zuwa Juma'a na tattaunawa kan batutuwan da suka shafi lamurran mata kamar girki, kwalliya, shafe-shafe, aure, ilimi, matsalar fyade, reno, shayarwa, kula da gida da makamantansu. Shirin na lale marhabin da ra'ayoyin masu sauraro daga kowacce kusuwar ta duniya. Kuna iya tuntubar wannan lambar ta manhajar WhatsApp domin shiga cikin shirin +2349088888990. Wannan shirin na hadin guiwa ne tsakanin Hukumar Raya Kasashe ta Faransa AFD da Sashen Hausa na Radio France International.