Isa ga babban shafi
Mu Zagaya Duniya

Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da dubu 9,000, fiye da rabinsu kuma mata ne da kananan yara

Wallafawa ranar:

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Zirin Gaza, tare da gargadin cewa lokaci na kurewa kasashe kan bukatar dakile yi wa Falasdinawa kisan kare dangi a yankin na Gaza.

Mutanen Gaza na neman yan uwan su yan lokuta biyo bayan harin Isra'ila
Mutanen Gaza na neman yan uwan su yan lokuta biyo bayan harin Isra'ila REUTERS - STRINGER
Talla

Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filpipo Grandi ya bukaci mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar da su kawo karshen rarrabuwar kawunan da ke tsakaninsu, don tabbatar da an tsagaita wutar da za ta dakatar da salwantar rayukan Falasdinawa a Zirin Gaza.

Wani Bafalasdine cikin jimami, bayan harin Isra'ila da ya kashe Falasdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke Zirin Gaza.
Wani Bafalasdine cikin jimami, bayan harin Isra'ila da ya kashe Falasdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke Zirin Gaza. REUTERS - Stringer .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.