Isa ga babban shafi

Kasashen Latin sun fusata da Isra'ila bayan kashe 'yan gudun hijira a Gaza

Kungiyoyin agaji da kasashe da dama sun yi Allah wadai da harin Isra’ila da ya kashe Falasdinawa akalla 100, tare da jikkata wasu daruruwa a sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a Zirin Gaza.

Daruruwan Falasdinawaa sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya, yayin kokarin tono 'yan uwansu da baraguzan gini suka danne, bayan harin bam din da Isra'ila ta kai kan sansanin mafi girma a Zirin Gaza.
Daruruwan Falasdinawaa sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya, yayin kokarin tono 'yan uwansu da baraguzan gini suka danne, bayan harin bam din da Isra'ila ta kai kan sansanin mafi girma a Zirin Gaza. © STRINGER / Reuters
Talla

Masu caccakar kasar ta Isra’ila dai sun bayyana cewar kamata yayi farmaki kan sansanin na ‘Jabaliya’ ya farkar da shugabannin kasashen duniya don tabbatar da tsagaita wuta a Zirin Gaza.

Daraktan Asibitin Indonesia da ke kusa da sansanin ya ce daga cikin wadanda suka mutu a harin har da iyalan wani dan Jarida da yawansu ya kai mutane 19.

Isra’ila dai na ci gaba da kai farmaki ta sama da kasa a yankin Zirin Gaza, tare da kaddamar da samame a wurare da dama a gabar Yamma da kogin Jordan, inda jami’na tsaronta suka kame Falasdinawa da dama.

Wani makami mai linzami da sojojin Isra'ila suka harba kan wani sashin yankin Zirin Gaza.
Wani makami mai linzami da sojojin Isra'ila suka harba kan wani sashin yankin Zirin Gaza. © JACK GUEZ / AFP

Rayuwa na dada yin kunci a Zirin Gaza

A halin da aka ciki, kamfanin sadarwa na yankin Falasdinu ya ce an katse intanet da layukan wayoyi a yankin na Gaza baki daya, matakin da wata kungiyar agaji ta bayyana a matsayin kokarin yin rufa-rufa kan laifukan yakin da Isra’ila ke aikatawa.

Ma'aikatar kiwon lafiyar yankin na Falasdinu kuwa, gargadi ta yi ga kasashe game da halin da asibitoci ke ciki na rashin makamashi, tana mai cewa nan da wani lokaci man fetur din da suke da shi zai kare, matakin da ke tattare da gagarumar barazana ga Faladinawa da suka jikkata, wanda adadinsu ya zarta dubu 20 a halin yanzu, sai kuma fargabar rasa jarirai bakwaini da ake lura da lafiyarsu cikin na’ura.

Shugaban kasar Bolivia Luis Arce.
Shugaban kasar Bolivia Luis Arce. © Juan Karita / AP

Kasashen Latin Amurka da dama sun fara daukar matakin yanke huldar diflomasiyya tsakaninsu da Isra'ila, inda Bolivia ta fara katse dangantaka da ita kan abin da ta kira laifukan yakiin da take aikatawa a Gaza.

Chile kuwa jakadanta da ke Isra'ila ta kira zuwa giida saboda cin zarafin fararen hular da Isra’ila ke yi, lamarin da  shugaban kasar ta  Chile  Gabriel Boric ya ce ba abin da zai lamunta bane. Tuni Colombia ma ta dauki matakin janye nata jakadan daga Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.