Bitar labaran mako- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da tarin daliban jami'ar Gusau
Wallafawa ranar:
Kunna - 20:07
Shirin Mu zagaya duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar kowanne mako ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muka yi bankwana da shi, inda a cikinsa za ku ji yadda 'yan bindiga suka sace gomman dalibai a Jami'ar tarayya ta birnin Gusau a jihar Zamfara.
Haka zalika a cikin shirinza ku ji yadda Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin daukaka kara bayan matakin kotun sauraren kararrakin zabe na kwace nasarar da ya yi a zaben watan Maris.
Bugu da kari shirin ya leka sauran sassan Duniya dauke da muhimman labarai na wannan mako, ciki kuwa har da dambarwar bakin haure a Italiya baya ga ziyarar Sarki Charles na 3 a Faransa baya ga ziyarar Fafaroma Francis.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu