Isa ga babban shafi
Mu Zagaya Duniya

Bitar labaran Mako; Yunkurin ECOWAS na daukar matakan soji a Nijar

Wallafawa ranar:

Cikin batutuwan da Shirin wannan mako ya waiwaya tare da "Nura Ado Sulaiman", akwai matakin da kungiyar Kungiyar ECOWAS ta dauka na amince wa da shirin kafa rundunar soji ta wucin gadi wadda za a yi amfani da ita wajen kai hari a kan sojojin da suka yi juyin Mulki a Nijar, idan matakan diflomasiya suka gaza haifar da ‘da mai ido.

Taron kungiiyar na ranar 30 ga watan Yulin 2023 da ya gudana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, game da makomar Nijar da ta fada hannun mulkin soji.
Taron kungiiyar na ranar 30 ga watan Yulin 2023 da ya gudana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, game da makomar Nijar da ta fada hannun mulkin soji. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Sakamakon takunkumai da suka hada rufe iyakoki, da kuma hana hada-hadar kudade da kasashen Yammacin Afirka suka kakaba wa Jamhuriyar Nijar, yanzu haka an fara fuskantar karancin naman kaji, kifi da ake shigar da su kasar.

A cikin shirin, akwai batun, mutanen da suka rasa ‘yan uwansu ko kuma suka samu raunuka a sanadiyyar harin ta’addancin da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Nairobin kasar Kenya a shekarar 1998, da suka bukaci Amurka ta biya su diyya, shekaru 25 bayan faruwar wannan lamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.