Malam Isa Sanusi kan warware rikicin ECOWAS da Nijar da Mali da Burkina Faso
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:33
Kungiyar ECOWAS na ci gaba da lalubo hanyar warware rikicin da ke tsakanin ta da kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina wadanda sojoji suka yi juyin mulki. Tuni kungiyar ta sanya musu takunkumin karya tattalin arziki, yayin da su kuma kasashen suka ce sun fice daga cikinta. A karshen wannan makon ne ake saran ECOWAS ta gudanar da taro na musamman domin nazari a kan rahotannin da take karba dangane da wadannan kasashe.
Dangane da wannan takun saka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daraktan Kungiyar Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sanusi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu........
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu