Isa ga babban shafi

Ministocin wajen kasashen ECOWAS na taro a Abuja kan rikicin siyasar yankin

Ministocin wajen kasashen yammacin Afrika na taro yau Alhamis a birnin Abuja na Najeriya don tattaunawa game da matsalolin da suka dabaibaye kasashen kungiyar musamman dambarwarta da kasashen yankin 3 da ke karkashin mulkin Soji.

Wani taron ECOWAS a Abuja.
Wani taron ECOWAS a Abuja. © KOLA SULAIMON / AFP
Talla

Taron na ECOWAS na zuwa a dai dai lokacin da shugaba Macky Sall ke fuskantar boren jama’ar kasar kan matakinsa na dage lokacin babban zaben kasar daga watan nan zuwa Disamba, batun da ‘yan adawa ke bayyanawa da juyin mulki.

A karshen watan jiya ne kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar suka bayyana shirin ficewa daga kungiyar sai dai ECOWAS ta ce takardun bukatar ficewarsu basu cika sharuddan da doka ta tanada ba.

Kwamitin tsaro na ECOWAS ya bayyana cewa tattaunawar ministocin wajen kasashen za ta mayar da hankali ne kan matsalolin siyasa da tsaro da suka dabaibaye kasashen yankin da kuma barazanar da ke tunkaro su musamman akan iyakokinsu da kasashen da ke karkashin mulkin Soji.

Shiga aamar sauti, domin sauraron rahoton Muhammad Sani Abubakar.

Babu dai tabbacin ko ministan wajen Senegal na cikin wadanda za su halarci wannan taro, dai dai lokacin da matsalar siyasar kasar ke cikin muhimman batutuwan da taron zai mayar da hankali akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.