Isa ga babban shafi

Muna bin matakan difulomasiya don warware matsalar juyin mulkin Nijar - Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewar, a matsayinsa na shugaban ECOWAS ya na daukar matakan bayan fage wajen warware matsalar juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar domin kaucewa zub da jini. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Tinubu ya shaidawa ministar harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna cewar Najeriya na bin abinda ke faruwa a Nijar sau da kafa da kuma daukar matakan diflomasiyar da suka da ce. 

Shugaban Najeriya ya bayyana jagoranci a matsayin daukar matakai dai-dai da bukatar jama’a da koke kokensu da kuma magance matsalolin da suka addabe su. 

"Najeriya ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar wanda ya shafi iyakokin jihohi guda 7, kuma wadannan jihohi na da al’ummomi sosai, saboda haka ina jagorancin ECOWAS ta hanyar da zamu kaucewa aiki cikin fushi wanda zai kaiga yin nadama". 

Tinubu ya ce akwai abokinsu kuma zababben shugaban kasa Bazoum Mohammed da sojoji suka yi garkuwa da shi, saboda haka ya zama wajibi su yi taka tsantsan domin kare lafiyarsa da ta iyalansa. 

Shugaban Najeriya ya ce ya fahimci cewar ‘yan Najeriya basa bukatar yaki a Nijar, amma hakan ba zai hana su daukar mataki mai karfi ba. 

Tinubu ya ce Najeriya za ta ci gaba da hada kan kawayen ta na duniya domin samo hanyoyin warware rikicin Nijar ta hanyar ruwan sanyi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.